VOOZH about

URL: https://www.trtafrika.com/hausa/article/a677203a8de5

⇱ Nijeriya ta kama mutane takwas saboda yaɗa labarai marasa tushe - TRT Afrika


| Hausa
| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta kama mutane takwas saboda yaɗa labarai marasa tushe
Gwamnatin Nijeriya ta kama aƙalla mutane takwas a 'yan makonnin nan saboda yaɗa labaran ƙarya a kafofin sada zumunta.
👁 Nijeriya ta kama mutane takwas saboda yaɗa labarai marasa tushe
Najeriya ta kama mutane takwas bisa zargin yada labaran karya. / Reuters

Hukumomin Nijeriya sun kama aƙalla mutane takwas a 'yan makonnin baya bayan nan saboda yaɗa bayanan ƙarya a kafafen sada zumunta, yayin da jami'ai ke yin barazanar tsaurara hukunci bayan yaɗuwar bayanan ƙarya da suka biyo bayan sace ɗalibai daga wata makaranta kwanan nan.

An sace ɗaliba ne a Jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Nijeriya a ranar 15 ga Mayu.

‘Yanbindiga sun saci aƙalla dalibai 46 da ma'aikata a harin da suka kai makarantu uku a jihar Oyo, abin da rundunar soji ta bayyana a matsayin harin ta'addanci.

Bayan ɗaliban sun shafe wata guda a hannun masu garkuwa, an fara yaɗa labaran ƙarya game da wannan lamari da ya ɗauki hankulan jama’a sannan aka ringa yaɗa su a kafafen sada zumunta. Ɗaya daga cikin ikirarin ƙaryar na cewa an kashe ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace.

Wallafe-wallafe 15 'masu ruɗani'

Mai magana da yawun 'yan sanda na Jihar Oyo, Olushola Alayande, ya shaida wa AFP cewa, 'Rundunar ta mayar da martani kan wallafe-wallafe masu ruɗani da ba su gaza 15 ba.'

''Wani salo da ake maimaitawa shi ne yaɗuwar iƙirarin da ke tayar da hankali, sake yaɗe bidiyo daga abubuwan da basu da alaƙa da lamarin, da kuma labaran shaci-faɗi da ake gabatarwa a matsayin gaskiya,'" in ji shi.

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN

Yada bayanan ƙarya kansa ma ya munana.

A Legas, cibiyar tattalin arziƙin ƙasar, gungun jama’a sun kashe wani mai babur mai shekaru 24 bayan yaɗuwar wani iƙirarin ƙarya cewa 'yanbindiga suna mamaye birnin. An kama mutane 15 bisa alaƙa da wannan lamari.

Shugaban ƙasa ma bai tsira ba daga labaran na karya

Sau da yawa ana yaɗa ƙirƙirarrun labarai marasa tushe a kan Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda ke neman wa'adi na biyu a zaben watan Janairu.

Masu nazari sun ce ƙaratowar zabe ta bai wa mutane ƙwarin gwiwa wajen ƙara yaɗa labaran ƙarya da karkatar da bayanai.

A kwanan nan rundunar soji ta musanta wani bidiyon da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar AI, wanda aka saka a Facebook, wanda ya yi iƙirarin nuna Hafsan Hafsoshin Ƙasar Olufemi Oluyede yana cewa ba shi da sauran dabarun magance matsalar rashin tsaro.

Yawancin waɗanda aka kama an tuhume su ne bisa Dokar Laifukan Intanet ta Najeriya (Cybercrimes Act), wadda ta haramta yaɗa bayanan ƙarya a kafafen sada zumunta tare da tanadin hukuncin ɗaurin shekaru uku ko tarar naira miliyan bakwai (kimanin dala 5,000).

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN
Rumbun Labarai