VOOZH about

URL: https://www.trtafrika.com/hausa/article/580c245be164

⇱ 'Yanwasa 14 daga gidaje 7 da ke buga Gasar Kofin Duniya - TRT Afrika


👁 'Yanwasa 14 daga gidaje 7 da ke buga Gasar Kofin Duniya
Désiré Doué da Guéla Doué sun fuskanci juna yayin da Faransa da Ivory Coast suka fafata a wasan sada zumunta gabanin gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026. / APA News Agency
'Yanwasa 14 daga gidaje 7 da ke buga Gasar Kofin Duniya
Wasu 'yanwasa 'yan gida-ɗaya kan bazama neman damarmakin shiga tawagar ƙasa-da-ƙasa, inda wasu kan zaɓi ƙasar da aka haife su, wasu kuma ƙasar iyayensu, har a ƙarshe 'yan-uwa ɗaya kan samu kansu a mabambantan tawagogi.
👁 Mazhun Idris
Mazhun Idris

A gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 da ke gudana a Amurka, Canada, da Mexico, akwai ‘yanwasa yan gida-ɗaya da ke buga gasar tare, wasu a tawaga guda, wasu kuma na wakiltar ƙasashe mabambanta. Ga labarin wasu cikin rin waɗannan ‘yanwasa guda 14.

Iñaki Williams da Nico Williams

Iñaki da Nico Williams sun girma tare a Sifaniya har suka buga wasa a Athletic Club, amma da suka tashi shiga tawagar ƙasa-da-ƙasa, sai suka raba gari.

Nico Williams ya zaɓi Sifaniya, shi kuma Iñaki ya shiga tawagar Ghana, ƙasar da aka haifi iyayensu, Félix Williams da María Arthuer. A yanzu haka, ‘yanwasan biyu suna buga wa ƙasashe biyu gasar Kofin duniya ta FIFA 2026.

Désiré Doué da Guéla Doué

Désiré da Guéla Doué ‘yan gida ɗaya ne da suka girma tare. Iyayensu ‘yan asalin Ivory Coast ne da suka yi hijira zuwa Faransa. Désiré da Guéla sun fara buga ƙwallo a Stade Rennais ta Faransa.

Désiré ya zama tauraro a PSG, sannan ya shiga tawagar Faransa. Shi kuwa Guéla, ya zaɓi buga wa Ivory Coast, kuma su biyun duka a halin yanzu suna buga gasar Kofin Duniya, amma sanye da mabambantan jesi.

 Derrick Luckassen da Brian Brobbey

Mahaifiyar Derrick da Brian Brobbey ta haife su a Netherlands, amma ubansu daban-daban. Sun fara ƙwallo tun suna matasa a Netherlands, amma sai suka zaɓi shiga tawagar ƙasa daban.

Brian Brobbey ya zaɓi buga wa tawagar Netherlands, yayin da Derrick Luckassen yake buga wa ƙasar da suke da tsatso, wato Ghana, kuma a yanzu sun haɗe a gasar Kofin Duniya.

 John Souttar da Harry Souttar

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN

An haifi John da Harry Souttar a Aberdeen, Scotland, kuma dukansu suna buga ƙwallo a matsayin masu tsaron baya.

Sai dai kasancewar suna da tsatson Scotland da Australia, John ya shiga tawagar Scotland, yayin da Harry yake wakiltar Australia, kuma har ya buga musu Kofin Duniya na 2022, kafin su haɗu a kakar bana.

Laros Duarte da Deroy Duarte

Laros da Deroy Duarte sun kwashe lokacinsu na ƙwallo a Netherlands, amma da lokacin shigarsu tawagar ƙasa ya yi, dukkansu sun zaɓi buga wa ƙasarsu ta asali, Cape Verde wasa.

Hasali ma, yawancin ‘yan tawagar ƙasar ta Cape Verde, wadda yanzu ake kira da Cabo Verde, a Netherlands suke taka leda.

Lucas Hernández da Theo Hernández

Lucas da Theo Hernández suna buga wa tawagar Sifaniya a tare, duk da cewa Lucas ne ya fara shiga tawagar, har ma ya ɗaga Kofin Duniya lokacin da Faransa ta lashe kofin a 2018.

A halin yanzu dai ‘yan gida ɗayan za su yi ƙoƙarin haɗa-kai don lashe gasar ta bana.

Leandro Bacun da Juninho Bacuna

Leandro da Juninho Bacuna na ƙasar Curaçao, ‘yan-uwa ne da suka girma a birnin Groningen na Holland.

Suna buga wa ƙasarsu Curaçao wasa, ƙasa mafi ƙankanta da ke buga gasar kofin Duniya, wanda kuma shi ne karonta na farko na shiga gasar.

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN
Rumbun Labarai