VOOZH about

URL: https://www.trtafrika.com/hausa/article/4bfdbb22893a

⇱ Kotun Nijeriya ta ba INEC umarnin soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu - TRT Afrika


| Hausa
| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Kotun Nijeriya ta ba INEC umarnin soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu
Mai Shari’a Peter Lifu, a cikin wani hukunci da ya yanke, ya umarci hukumar INEC da ta soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa saboda sun kasa samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a babban zaɓen da ya gabata, kamar yadda doka ta tanada.
👁 Kotun Nijeriya ta ba INEC umarnin soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu
INEC / Nigerian Government

Kotun Tarayyar Nigeria ta bayar da umarnin soke rajistar Jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu kan samunsu da laifin ƙin cika wasu matakai da kundin tsarin mulki ya buƙaci jam’iyyu su cika.

Wani alkalin Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a Peter Lifu, a cikin wani hukunci da ya yanke, ya umarci hukumar INEC da ta soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa saboda sun kasa samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a babban zaɓen da ya gabata, kamar yadda doka ta tanada.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa jam’iyyun siyasar biyar da hukuncin ya shafa sun haɗa da African Democratic Congress, Accord, Action Alliance, Action Peoples Party da Zenith Labour PartyThe News Agency of Nigeria (NAN) reports that the five political parties include ADC, Accord (A), Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP) and Zenith Labour Party (ZLP).

Mai Shari’a Lifu, wanda tun da farko ya yi watsi da duk ƙorafe-ƙorafen farko da waɗanda ake ƙara suka shigar, ya kuma umarci INEC da kada ta bari waɗannan jam’iyyu su shiga zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban zaɓen shekarar 2027, saboda sun gaza cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya gindaya.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN ya ce wata ƙungiya mai suna Incorporated Trustees of the National Forum of Former Legislators ce ta shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026 a kan jam’iyyun siyasar biyar.

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN

Mai ƙarar, wanda ya kuma haɗa da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a cikin shari’ar, ya sanya INEC a matsayin wadda ake ƙara ta farko.

Ƙungiyar ta kafa hujjar cewa jam’iyyun da abin ya shafa sun kasa cika sharuddan kundin tsarin mulki da suka shafi yawan ƙuri’u da kuma yadda suka taka rawa a zaɓe.

Ta ce doka ta tanadi cewa jam’iyyun siyasa dole ne su samu aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a zaɓukan da aka ayyana domin su ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar ƙasa.

Saboda haka, ta roƙi kotun da ta ba da umarnin soke rajistar jam’iyyun, tana mai jaddada cewa babu ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara da ya gabatar da hujjojin da suka rushe dalilan da ta gabatar.

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN
Rumbun Labarai