VOOZH about

URL: https://www.trtafrika.com/hausa/article/8641ad0d4589

⇱ Sojojin Nijeriya sun ceto mutum hudu da aka sace daga gungun 'yanta'adda a Katsina - TRT Afrika


| Hausa
| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum hudu da aka sace daga gungun 'yanta'adda a Katsina
Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa mutanen sun samu raunukan bindiga yayin da suke tsare, amma an fara ba su kulawar lafiya nan-take bayan ceton su.
👁 Sojojin Nijeriya sun ceto mutum hudu da aka sace daga gungun 'yanta'adda a Katsina
Sojojin Nijeriya suna samun nasara kan 'yanta'adda a baya-bayan nan. / Reuters

Hukumomin jihar Katsina a arewacin Nijeriya sun sanar da ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a jihar, bayan wani farmaki da sojojin ƙasar suka yi kan gungun wani riƙaƙƙen ɗanfashin daji.

Ana zargin gungun Kachalla Muhammadu Fulani, wani ɗanfashin daji da ake nema ruwa a jallo, da kai jerin hare-hare da sace mutane a jihar da ke fama da rashin tsaro.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gina na Jihar Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, shi ne ya fitar da sanarwar, inda ya bayyana sunayen waɗanda rundunar sojin da ceto kamar haka: Musa Yakuba, Sa’adu Dayi, Mukhtar Danja, da Salisu Danja.

Sanarwar ta ƙara da cewa, nasarar ceto mutanen na zuwa ne yayin da ake tsananta kai samame a wuraren da ake zaton maɓoyar ‘yanta’adda ce.

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN

Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa mutanen sun samu raunukan bindiga yayin da suke tsare, amma an fara ba su kulawar lafiya nan-take bayan ceton su.

Haka nan gwamnatin Katsina ta jinjina wa Sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro da suka aiwatar da aikin ceto, yayin da ta jaddada aniyar kamo Kachalla Muhammadu Fulani.

Sojojin Nijeriya suna samun nasara kan 'yanta'adda da masu aikata manyan laifuka a ƙasar, musamman a baya-bayan nan bayan sun tsananta kai musu farmaki.

ZA KU SO WAƊANNAN
ZA KU SO WAƊANNAN
Rumbun Labarai